Kansar Hanji wata mummunar cuta ce da ake fama da ita a cikin ciki. Cutar ta fi bayyana a lokacin da mutum ya haura shekara talatin zuwa sama. Takan yi sanadiyyar rasa rayuka da dama a kowace shekara, don haka, yana da kyau a kula sosai, sannan a dauki matakan kariya domin inganta lafiya. Ga wasu daga cikin hanyoyin da ake bi domin kauce wa hadarin Kamuwa da cutar:
1. Ka ƙara Yawan Cin Abinci Mai Dauke da Sinadarin Fiber.
Cin hatsi, kamar dawa, gero, shinkafa, doya, rogo, dankalin hausa. Da sauransu. Sai su alayyahu, kuɓewa da sauransu. Sannan a riƙa amfani da kayan itace irinsu ayaba, piya, lemon zaƙi, abarba da dai sauransu.
Fiber yana taimakawa wajen fitar da datti da gubobi daga hanji kafin su lalata shi.
Za a iya ƙara bincike a kan ire-iren abinci masu ɗauke da wannan sinadarin
2. Rage Cin Processed Foods
Noodles, sausage, biredi da dai sauransu suna ƙara haɗarin ciwon daji, saboda preservatives da nitrates da suke ɗauke da shi.
3. A Guji Zama Ba Tare Da Motsa Jiki Ba
Motsa jiki sau 3-5 a mako yana taimakawa wajen daidaita narkewar abinci da rage kumburin jiki wanda ke da alaƙa da ciwon hanji.
4. Daina Shan Taba da Giya
Waɗannan abubuwa suna lalata DNA na ƙwayoyin hanji, suna ƙara haɗarin mutation da ciwon daji.
5. Yin gwaji musamman in akwai ɗan uwanka da ya taɓa fama da ita.
Idan kana da shekaru 35 sama, ko kuma akwai wani wanda ya yi fama da ciwon daji a dangi, ka riƙa yin colonoscopy ko stool occult blood test duk shekara. Gano ta da wuri na iya ceton rayuwarka! Allah shi ba mu lafiya, amin.
