Wasu Daga Cikin Bukatun Nijeriya Ga Majalisar Dinkin Duniya


Wakilin Nijeriya, mai girma tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Borno, mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya mai ci yanzu Kashim Shetima, wanda ya wakilci Shugaban ƙasa mai girma Bola Ahmad Tinubu a taron majalisar ɗinkin duniya karo na 80.

A filin taron malam Shetima, ya nemi da majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da ta ba wa Nijeriya kujerar dindindin ta kwamitin tsaro, duba da irin ɗumbin gudunmuwar da ƙasar ke bayarwa a ɓangaren harkar tsaro a nahiyar Afirka da ma duniya bakiɗaya, ga kuma tarin yawan jama'a masu albarka da ƙasar ke alfahari da shi.

Ya ƙara da cewa, ''Majalisar Ɗinkin Duniya ya kamata ta samar da ƙasar Falasɗinu a gaske ba wai kawai a takardu da ƙudiri ba, tare da kawo ƙarshen rikice-rikicen da ƙasashen duniya ke fama da shi.''

 Mataimakin shugaban ƙasar, ya ƙara da cewa. ''Majalisar Ɗinkin Duniya ya kamata ta ɗauki matakin rage basussukan da suka zame wa ƙananun ƙasashe masu tasowa ƙarfen ƙafa, ba tare da nuna an ba su sadaka ba, sai dai kawai don neman zaman lafiya da wadata dukkan ɓangarorin ƙasashe.'' Ya ƙara da cewa. ''Ba daidai ba ne zura idanun da aka yi ga ƙasar Isra'ila akan irin harin da ta yi wa Qatar, kuma ya kamata a samu hanyar hana faruwar irin wannan a gaba.''

Post a Comment

Previous Post Next Post