Barayin Waya Sun Addabi Katsina

 A baya bayan nan, tun lokacin da ɓarayin waya suka fara shiga halin ƙunci da wahala a Kanon Dabo, wanda fusatattun matasan Kanon suka riƙa duka har ma da ƙona ababen hawan masu ƙwacen wayar a kasuwanni da unguwanni cikin ƙwaryar Kano da kewaye, sun samu sauƙi sosai na sace-sacen wayar. Sai dai a jihar Katsina kuma yanzu abin ya zama tamkar gasa.

A yammacin Talatar da ta gabata ne aka samu wasu ɓarayin waya suka samu wani matashi mai suna Auwal suka soke shi da wuƙa a muƙamuninsa sannan kuma suka yi abin gaba da wayar tasa suka barshi kwance cikin jini.

Wannan al'amarin ya faru ne a wani ɓangare na unguwar Tsohuwar Kasuwa da ke cikin birnin Katsina.

Faruwar hakan ke da wuya a jiya Laraba majalisar dokoki ta jihar ta amince da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama da laifin ƙwacen waya ta amfani da makami, ƙudurin da Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Honourable Aliyu Abubakar Albaba ya gabatar.

Post a Comment

Previous Post Next Post