Kotu Ta Umurci a Daura Aure Tsakanin Ashiru Mai-Wushirya Da Masoyiyarsa Cikin Kwanaki 60

 

Mai-Wushirya

Wata kotu a jihar Kano ta bayar da umarni cewa a daura aure tsakanin Ashiru da masoyiyarsa cikin kwanaki 60 daga yau. Wannan hukunci ya zo ne bayan kotun ta saurari ƙarar da ta shafi dangantakar su da kuma muhawara da ta biyo baya a kafafen sada zumunta.

Kotun ta kuma umurni hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da ta sanya ido wajen tabbatar da cewa an aiwatar da wannan auren yadda doka ta tanada, domin kaucewa wata matsala a nan gaba.

Rahotanni sun nuna cewa wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, musamman a shafukan sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan hukuncin, yayin da wasu ke ganin bai kamata kotu ta tsoma baki a soyayya ba.

Yanzu dai mutane da dama suna jiran ganin ko za a cika umarnin kotun cikin wa’adin da aka bayar.

Me kuke fata ga Ashiru da masoyiyarsa?

Ku bayyana ra’ayinku a ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post