NAHCON Ta Yabi Tinubu Da Shettima Kan Umarnin Rage Farashin Hajjin 2026
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima bisa umarnin da suka bayar na rage farashin kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayar da wannan umarni a wani taro da ya gudanar da shugabannin hukumar NAHCON a ranar Litinin, bisa umarnin Shugaban Ƙasa, inda ya buƙaci hukumar ta rage kuɗin cikin kwanaki biyu.Tun da farko, NAHCON ta sanar da cewa maniyyata daga Arewacin Najeriya za su biya Naira miliyan 8.2, yayin da na Kudu za su biya Naira miliyan 8.5.
A wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Sadarwa da Wallafa ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a madadin hukumar, NAHCON ta bayyana cewa umarnin Shugaban Ƙasa ya nuna gwamnati mai sauraron jama’a da fahimtar ƙalubalen tattalin arziki da musulmi ke fuskanta wajen shirin aikin Hajji.
Hukumar ta kuma yaba da shawarar gwamnatin ga maniyyata da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da su yi biyan kuɗi da wuri, domin amfana da ƙarfafa darajar Naira. Wannan mataki, in ji hukumar, zai taimaka wajen rage nauyin kuɗi da kuma tabbatar da ingantaccen shiri kafin tafiya.
NAHCON ta bayyana cewa umarnin na gwamnatin Tarayya ya nuna jajircewar Shugaba Tinubu wajen inganta tsarin aikin Hajji a ƙasar, ta hanyar samar da sauƙi, gaskiya da ingantaccen tsari.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da duk masu ruwa da tsaki domin aiwatar da wannan umarni yadda ya kamata, don tabbatar da cikakken shiri da tafiyar Hajji mai albarka a shekarar 2026.
NAHCON ta kuma buƙaci maniyyata su gaggauta biyan kuɗinsu, tana mai tabbatar da cewa sabbin farashin da aka rage za su fito nan ba da jimawa ba.