Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Adams Oshiomhole, ya yi raddi ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, yana mai cewa ba su da wata dama ta cin zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
Tsohon gwamnan Edo ya ce Atiku da Obi waɗanda yanzu suka haɗu a jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) suna da tarihin ƙasa a zaɓe, duka lokacin da suka tsaya tare da kuma lokacin da suka tsaya dabam.
“Atiku da Obi ba su taba yin nasara ba. Shin ba tare suka tsaya a baya suka fafata da APC ba? Kuma aka kayar da su?” in ji Oshiomhole. “Ko da suna son su haɗa kowane ƙarfi ne, gaskiyar ita ce: lokacin da suka tsaya tare, APC ta kayar da su ƙwarai.”
Ya ƙara da cewa sakamakon zabukan baya ya nuna babu abin da zai canza idan suka sake haɗuwa.
“Suna da tarihi na faduwa tare, suna da tarihi na faduwa dabam. Don haka idan suka sake haɗuwa, za su sake faduwa,” in ji shi.
A tunawa, Atiku shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, yayin da Obi ya tsaya ƙarƙashin Labour Party (LP). Dukansu sun samu jimillar kuri’u sama da miliyan 12, inda suka ƙare a matsayi na biyu da na uku a bayan Shugaba Bola Tinubu na APC.
Sabuwar haɗin kansu a karkashin ADC ta tayar da jita-jitar yiwuwar tsayawa takara tare a 2027 — abin da Oshiomhole ke ganin zai sake kai su ga rashin nasara daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.