ASUU Ta Fara Shirye-shiryen Yajin Aikin Gargadi Na Kasa

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta fara shirye-shiryen yajin aikin gargaɗi na ƙasa baki ɗaya. Wannan na zuwa ne yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta ba Gwamnatin Tarayya ke gab da ƙarewa.

AsuuA wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Farfesa Christopher Piwuna, ya sanya hannu a kai, ASUU ta nuna rashin gamsuwa da shiru da rashin jajircewar gwamnati wajen warware matsalolin da ke addabar jami’o’i.

Ƙungiyar ta ce wa’adin na da nufin tilasta gwamnati ta rattaba hannu da aiwatar da yarjejeniyar da aka kammala tun watan Fabrairu, 2025.

Farfesa Piwuna ya ce mako guda bayan sanar da gwamnati, babu wani ci gaba da ya cancanci a yaba. Ya kuma buƙaci mambobin ASUU su ƙara kaimi wajen shirye-shirye da haɗin kai domin ɗaukar matakin gaba.

Ya jaddada cewa haɗin kai ne makamin kungiyar wajen kare muradunta da farfado da tsarin jami’o’in ƙasar domin ya zama mai gogayya a matakin duniya.

ASUU ta kuma umarci mambobinta da su rika bin jagorancin shugabannin rassansu da halartar tarurrukan ƙungiyar domin samun sabbin bayanai.

Post a Comment

Previous Post Next Post