Tinubu Ya Umurci NAHCON Da Ta Sake Duba Farashin Kujerar Hajjin 2026

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya umurci Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ta fito da sabbin farashin kujerun aikin Hajjin shekarar 2026 cikin kwana biyu, bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na yin gaggawar sake duba farashin.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taro da ya gudanar tare da shugabannin hukumar NAHCON da mambobin kwamitin gudanarwarta a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Ya ce matakin ya zama dole ne sakamakon ci gaba da ƙaruwar darajar Naira a kan Dalar Amurka — wanda shi ne babban abin da ke tasiri wajen ƙididdige farashin aikin Hajji.

A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Stanley Nkwocha, ya fitar, Mataimakin shugaban ƙasa ya buƙaci haɗin kai tsakanin jami’an tarayya da na jihohi, ciki har da gwamnoni, wajen tsara da amincewa da sabbin farashin da suka dace.

Ya kuma buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da biyan kuɗaɗe da tura su cikin lokaci zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN) domin samun gudanar da aikin Hajji ba tare da tangarɗa ba.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan taron, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadeija, ya ce taron ya gudana ne domin kammala shirye- shirye na aikin Hajjin 2026, musamman wajen tantance sabon farashin kujeru.

Ya bayyana cewa burin gwamnati shi ne rage nauyin kuɗi da masu niyyar tafiya Hajji za su biya, bisa yanayin tattalin arzikin kasar da ke samun sauyi ta sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki na gwamnatin Tinubu.

Ya ce, “Farashin musayar kuɗaɗe na ƙara ingantuwa, inda darajar Naira ke ƙaruwa sakamakon tasirin gyare-gyaren tattalin arzikin Gwamnatin.

“Mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa idan alhazai sun biya kusan Naira miliyan 8.5 zuwa 8.6 a bara saboda matsin musayar kuɗi, yanzu da Naira ta ƙara ƙarfi, dole ne a sauƙaƙa kuɗin domin alhazai su amfana.

“Don haka an umurci hukumar NAHCON da ta koma ta sake duba sabon farashin da ya fi dacewa da yanayin musayar kuɗi na yanzu. Idan abin ya tafi yadda ake fata, za a samu gagarumin ragin kuɗi.”

Shi ma Sakataran NAHCON, Dokta Mustapha Mohammad, ya ce umarnin shugaban kasa zai karfafa yawan musulmai masu niyyar zuwa aikin Hajji a bana.

Ya ce, “Wannan ci gaba ne mai kyau. Mafi ƙarancin farashi zai ba wa musulmai da dama damar gudanar da wannan muhimmin rukuni na addinin Musulunci. Don haka, kamar yadda aka umurce mu, za mu yi aiki tuƙuru cikin waɗannan kwanaki biyu domin rage farashin zuwa mafi sauki da kowa zai iya biya.”

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi kuma Mataimakin Shugaban ƙungiyar Shugabannin Hukumar Alhazai ta Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Alhaji Faruk Aliyu Yaro, ya bayyana farin cikinsa da wannan mataki.

Ya ce, “Muna matukar farin ciki da wannan shiga tsakani da Shugaban ƙasa da Mataimakin shugaban ƙasa suka yi. Mun gode Allah da wannan umarni wanda tabbas zai rage kuɗin tafiya Hajji. Muna farin ciki sosai,” in ji shi.


Post a Comment

Previous Post Next Post