Asalin ranar ban tsoro idan an koma tarihi yana da alaka da tsohon tarihin bikin Maguzanci na Celtic (Wata Kabila ce ta Turawa) da aka fi sani da Samhain, wanda ake gudanarwa a ranar 1 ga Nuwamba a kalandar zamani.
Celtic sun gaskata cewa a dare kafin sabuwar shekara, iyakar da ke tsakanin duniyar masu rai da matattu ta na yin duhu.
A daren Oktoba 31 suna yin bikin Samhain, wanda daga baya ya zama (Hallowen), lokacin da aka yi imani cewa fatalwar matattu tana sato jiki ta sake dawowa duniya. Don haka mutane sukan sa tufafi kuma su na kunna wuta don tsoratar da fatalwoyin mamatan.
Bikin Halloween ya kasance fiye da shekaru dubu. Daga Baya ya zama biki na addini, bayan ya zama ruwan dare gama-gari tsawon shekaru har yin sa ake domin addini ya bace. A yau ana daukar Halloween a matsayin biki don sa sutura da nishaɗi, musamman ga yara.
A ƙarni na 7, Paparoma Boniface IV ya kirkiri ranar Waliyyai, wadda aka fara yi a ranar 13 ga Mayu. Bayan Ƙarni 1 Paparoma Gregory III ya mayar da ranar waliyan zuwa ranar 1 ga Nuwamba, wataƙila da nufin bikin Kirista ya maye gurbin bikin arna na Samhain, ranar ta koma ranar bikin tsarkaka (Waliyyai), wanda a lokacin ya zama sananne da Sunan (All Hallows Eve) ko (Halloween).
Ko da yake ya soma biki a yankunan Celtic na Ireland, ingila, da Faransa, da sauri ya bazu zuwa sauran sassan duniya.
Kiristoci masu ra'ayin yan mazan jiya sun hana yan mulkin mallaka na farko a Amurka a New England su yi bikin saboda ya sabawa addinin Kirista, su na Ganin Ya qamo asaline daga Maguzanci.
JI DA KYAU
Kalmar "Halloween" ta fito ne daga All Hallows' Eve, kuma tana nufin "maraice mai tsarki." Tarihin Halloween ya samo asali ne daga bikin arna da ake kira Samhain, shekaru ɗaruruwa da suka wuce. Kafin Paparoma Gregory III ya mayar da ranar ta zama ranar waliyyai tsarkaka (Halloween).
Ana bikin Halloween ne a ranar 31 ga Oktoba kowace shekara. A wannan shekarar ma za a yi bikin ranar 31 ga Oktoba.
