Tinubu Ya Soke Yafiyar Maryam Sanda, Ya Mayar Da Hukuncin Kisa Zuwa Shekaru 12 a Gidan Yari

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soke yafiyar da aka bai wa Maryam Sanda, wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello. A sabon matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka, an mayar da hukuncin kisan nata zuwa ɗaurin shekaru 12 a gidan yari.

Wannan na ƙunshe ne a cikin sabuwar takardar gwamnati (gazette) da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.

A cewar gazetten, Sanda ta shafe kusan shekaru shida da watanni takwas a gidan gyaran hali na tsaka-tsaki da ke Suleja, Jihar Neja, kafin sabon hukuncin ya amince da rage mata azabar daurin rai da rai bisa dalilan tausayawa. Wannan na nufin yanzu za ta ci gaba da zaman gidan yari na kusan shekaru biyar da watanni huɗu kafin ta samu 'yanci gaba ɗaya.

A cikin ƙarin jerin sunayen da fadar shugaban ƙasa ta fitar, an tabbatar da cewa hukuncin kisan Maryam Sanda an sauya shi zuwa ɗaurin shekaru 12 kacal, wanda ke barin saura mata ƙasa da shekaru shida a gidan yari.

Haka kuma, sama da mutane 80 da ke da laifuffuka daban-daban sun shiga cikin sabuwar jerin sunayen da aka sabunta, inda aka rage musu tsawon zaman gidan yari domin ba su damar sake farawa cikin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post