Wata Asibiti A Kasar Saudiyya Ta Yi Nasarar Cire Kansar Kwakwalwa Ta Hanyar Amfani Da Kirkirarrar Basira

 Ƙasar Saudi Arabia ta zama ƙasa ta farko da ta yi nasarar cire kansar ƙwaƙwalwa ta hanyar amfani da fasahar mutum-mutumi (AI). Wani asibiti a Riyadh kwanan nan ya yi nasara a karon farko ta hanyar cire kansar (cikin-ƙwaƙwalwa) ta hanyar amfani da dabarar mutum-mutumi (AI). Wannan ya bayyana a matsayin cigaba na baya-bayan nan da ake magana a kai a cikin shafin yanar gizon. 

Asibitin Saudiyya

A ranar 20 ga Oktoba, 2025, Asibitin ƙwararru na Sarki Faisal da Cibiyar Bincike (KFSHRC) da ke Riyadh sun sanar da cewa sun yi nasarar yin aiki irinsa na farko a duniya.

An yi aikin na tsawon sa’a ɗaya ne a kan wani dattijo mai shekaru 68. Yin amfani da mutum-mutumi, wanda babban tsarin lura ne na 3D ya jagoranta, ya ba da damar cire ƙwayar cuta mai tsawon santimita 4.5.

An sallami majiyacin a cikin sa'o'i 24, wanda hakan ya fi sauri wajen farfadowa fiye da yadda aka saba gani.

Post a Comment

Previous Post Next Post