Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito cewa Ƙungiyar Al-Qaeda ta yankin Sahel, wadda ke mubaya'a ga ƙungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta fitar da sanarwar da a ciki ta yi iƙirarin samun nasarar "kai hari kan shingen jami'an tsaron Najeriya'' a wani yanki da alamu suna nuna a yankin jihar Kwara ne da ke maƙwabtaka da bakin iyakar Benin.
Wannan ne karon farko da JNIM ta yi iƙirarin ɗaukar nauyin kai hari a Najeriya.JNIM ta fitar da sanarwar ce a kafarta ta al-Zallaqa a ranar 22 ga watan Nuwamba, duk da cewa ƙungiyar ba ta fitar da cikakken bayani kan harin ba, sannan ba ta bayyana haƙiƙanin inda ta kai harin ba, sannan ba ta bayyana adadin waɗanda harin ya rutsa da su ba.
Sai dai ta ce harin ya auku ne a wani ƙauye da ta kira da Larabci da "Duruma" a jihar da ta kira da "Tinkandu" wanda ke nufin garin bakin iyaka na Chikanda.
Sai dai rahotanni na cewa Duruma wani ƙauye ne da ke bakin iyakar Najeriya da Benin a ƙaramar hukumar Baruten da ke jihar Kwara.