Amurka Za Ta Tallafa Wa Najeriya A Fannin Tsaro'

Fadar shugaban Najeriya ta ce hukumomin Amurka sun ce za su tallafa wa ƙasar domin yaƙi da matsalar tsaron ƙasar.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce gwamnatin Amurka ta tabbatar da shirinta na zurfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da Najeriya.

Bayo ya ce taimakon ya haɗa da samar da ingantattun fasahohin leƙen asiri, da kayayyakin tsaro, da kuma sauran bayanai da za su ƙarfafa ayyukan da ake yi na yaƙi da ƴan ta'adda da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a ƙasar.

Matakin na zuwa ne bayan ganawar da aka yi a makon jiya tsakanin wata tawagar manyan jami'an Najeriya da jami'an Amurka.

Ƙasashen biyu sun amince da ƙarfafa dangantakar tsaro da kuma lalubo sabbin hanyoyin haɗin gwiwa.

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce tawagar Najeriyar, ƙarƙashin jagorancin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ta gana da manyan jami'an majalisar dokokin Amurka, da ofishin kula da harkokin addini na fadar White House, da ma'aikatar harkokin wajen Amurka, da majalisar tsaro ta kasa, da kuma ma'aikatar tsaro.

Tawagar Najeriyar ta ƙaryata zargin kisan kiyashi da ake yi a Najeriya, inda ta jaddada cewa munanan hare-hare na shafar iyalai da al'ummomi daban-daban.

Tawagar ta kuma yi watsi da irin kalaman da ake amfani da su wajen siffanta lamarin, inda ta ce irin wannan abu zai iya raba kan ƴan Najeriya ba, tare da gurɓata haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasa.

A cewar Mallam Nuhu Ribadu, ƙasashen biyu sun amince da aiwatar da wani tsarin haɗin gwiwa cikin gaggawa, da kuma kafa ƙungiyar haɗin gwiwa don tabbatar da tsarin bai ɗaya na haɗin gwiwa a ɓangarorin da aka cimma matsaya a kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post