Gwamnatin Najeriya ta ɗauki sabon mataki mai muhimmanci, bayan ganawar sirri da aka gudanar a makon jiya tsakanin wata tawaga ta manyan jami’an Najeriya da takwarorinsu na Amurka.
A cewar majiyoyi daga gwamnatin tarayya, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan harkokin tsaro, yaki da ta’addanci, da kuma ƙarfafa hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. An ce Amurka ta nuna sha’awar ƙara tallafawa Najeriya musamman a ɓangaren kayan aikin tsaro da horaswa.
Majiyar ta tabbatar da cewa wannan sabon matakin da Najeriya ta ɗauka yana cikin jerin matakan da ake son aiwatarwa domin inganta tsaro, magance kalubale a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, da kuma tabbatar da cewa rundunonin tsaron ƙasar na aiki bisa tsarin zamani.
Wata majiya daga fadar gwamnati ta shaida cewa gwamnati na fatan wannan haɗin gwiwa zai kawo gagarumin sauyi wajen yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke barazana ga kasar.
A halin da ake ciki, an ce za a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da fatan fitar da cikakken tsarin aiki nan ba da jimawa ba.