Al'ummar yankin Gama-giwa da Kewaye ta ƙaramar Hukumar Maradum da ke Jihar Zamfara, Sun koka yadda wani jagora 'yanbindiga yake musguna musu gami da ƙaƙaba musu harajin maƙudan kuɗaɗe, bayan da suka gama yi mashi noman damuna baki ɗaya.
Kamar yadda aka wallafa a shafin Yarima BK Dtm dake kafar Fezbuk, yanzu haka wani jagoran 'yanbindiga ya ɗora wa mazauna kauye a jihar Zamfara harajin Naira Miliyan 50 kuma ya ce nan da sati ɗaya yake buƙatar su haɗa mashi kuɗaɗen, haka kuma ya tabbatar masu da cewa duk 'yan ƙauyen da ba su yi saurin kawo kuɗin ba, za su fuskanci hukunci.
Al'ummar yankin sun tabbatar da rashin imanin jagoran 'yanbindigar da yaransa, sam ba su ɗauki rayuwar ɗan'Adam a bakin komai ba. Wannan ya sa suke mashi duk abunda yake buƙata dan dole.
