Amarya Ta Wa Ango Yankan Rago Kwana Hudu Da Daura Masu Aure

Wannan mata da miji ne da aka daura aurensu, bayan kwana hudu da daura auren a garin Jibia da ke Jihar Katsina, jiya Lahadi mijin yana bacci a daki da rana matar ta dau wuka ta masa yankan rago wanda ya yi sanadin rasa rayuwarsa nan take.

Amarya da Ango

Kamar yadda aka bayyana a shafin Fezbuk na Datti Asalafy da kuma Alhassan Mailafiya, akwai alamomi da yawa da suke nuna cewar mijin matar ya yi ganganci, an ce wannan hoton sun dauke shi ne bayan daura aure, ga sako nan a fuskarta ya bayyana a fili ba ta son mijin da aka aura mata.

Irin wannan ganganci  ne maza suke yi. Ko da wasa kar ka yadda ka auri macen da ba ta son ka domin kauce wa halaka. Mata suna nan da yawa a gari sai wadda ka zaba, don me za ka makale wa wacce ba ta son ka. Allah Ya jikansa da rahama, amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post