Tsohon sanata a shiyyar Daura zone, Senator Ahmad Babba Kaita ya bayyana damuwarsa game da satar dalibai da ake fama da ita a Nijeriya. Ga abinda ya wallafa a shafinsa na Fezbuk: Sace-sacen dalibai da aka gani a wasu daga cikin jihohinmu abin takaici da tayar da hankali ne ƙwarai.
Wannan yanayi da aka shiga ya sa wasu gwamnonin rufe makarantu. To amma abin tambaya shi ne rufe makarantu ita ce kawai mafita?
A ƙashin gaskiya tinkarar matsalar tsaron da muke fama da ita ta hanyar karya ƙashin bayan ‘yan bindiga ita ce hanyar da za a bi wajen sama wa mutane sauki.
Ya zama wajibi gwamnonimu su ɗaura ɗamara ta yaƙi da tsaro a jihohinmu, saboda haƙƙi ne da ya rataya kansu don ko a lokacin da suka sha rantsuwar kama aiki sai da suka yi alƙawarin kare rayuka da dukiyar al’umma.
GA SHI ABIN YA GAGARE SU …
