Fitaccen Jarumin Indiya Dharmendra Ya Rasu Bayan Doguwar Jinya

 An tabbatar da rasuwar gwarzon fina-finan Bollywood, Dharmendra, bayan wani lokaci da ya dauka yana fama da jinya. Marigayin, wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana taka rawa a masana’antar shirya fina-finai ta Indiya, ya kasance ɗaya daga cikin tsofaffin jarumai mafi shahara a tarihin Bollywood.

Dharmendra

Dharmendra ya fara haskawa a shekarun 1960, kuma tun daga wannan lokaci ya riƙa bayyana a cikin fitattun fina-finai da dama, ciki har da:

1. Sholay

2. Phool Aur Patthar

3. Yaadon Ki Baaraat

4. Dharam Veer

Salon aikinsa ya sa aka fi kiransa “He-Man of Bollywood”, saboda jarumtarsa da rawar da yake takawa a fina-finan faɗa da ban tsoro.

Rasuwarsa ta jawo gagarumin alhini a fadin Indiya da kasashen da ake kallo Bollywood, musamman ma a Afirka inda ya yi suna sosai.

Masoyan fim sun bayyana cewa Dharmendra “ya kasance jarumin da ya girma tare da su”, domin fina-finan sa sun nishadantar da gidaje da al’ummomi na tsawon shekaru aru-aru.

’Ya’yansa, ciki har da fitattun jarumai Sunny Deol da Bobby Deol, sun bayyana cewa sun rasa “tushen gidan su da ginshikin rayuwar su”.

Shahararrun ‘yan fim da dama sun kai gaisuwar ta’aziyya, suna yabon gagarumar rawar da Dharmendra ya taka wajen gina tarihin Bollywood tun shekaru da dama.

Dharmendra ya bar tarihi mai nauyi a masana’antar, inda ya fito a cikin fina-finai fiye da 100, kuma salon aikinsa da halayyarsa sun sa ya zama abin koyi ga sabbin jarumai.

Post a Comment

Previous Post Next Post