Ba Ita Ta Kashe Shi Ba
Wani sabon bayani da Datti Assalafi ya wallafa a shafinsa, ya tabbatar da cewa, a wata fira da ya yi da ahalin wanda aka kashe, ya bayyana masa cewa ba ita ta kashe shi ba, domin ita ce ma ta fito cikin gari tana ihun neman taimako kafin daga bisani ta kiɗime.
Ya ci gaba da cewa, bincike ne kaɗai zai fito da gaskiyar wanda ya kashe shi. Sai dai an fi danganta zargin da tsohon mijinta da ta baro gidansa ta auri wannan da aka yi wa yankan rago.
A firar ta su, ya bayyana cewa, auren soyayya suka yi ba na ƙiyayya ba, kamar yadda ake ta yamaɗiɗi tare da kafa hujja da hotunan jikinsu. An tabbatar masa da irin tsagwaron soyayyar da suka sha, kafin ta yi aurenta na fari, wanda ake zaton ma ta lashe auren nata ne, saboda soyayyar da take yi masa.
An jaddada masa cewa, kafin a yi masa yankan rago, sai da aka caccaka masa wuƙa a cinya, bayan da jini ya ɗebe sa ne, aka yi masa yankan rago. Hakan kuwa ya faru ne, jim kaɗan bayan dawowarsa gida sakamakon makullan shagonsa da ya manta. Shigowarsa gidan sai ya yi arba da wani ƙato a gidansa, wanda shi ne ake zargi da kashe shi.
Za a iya gane wanda ya yi aikin kisan ne kawai ta hanyar bayar da shaidar matarsa ko kuma ta hanyar ɗaukar samfurin hoton hannun da yake a jikin wuƙar da aka yi masa wannan ɗanyan aikin.
Muna addu'ar Allah ya karɓi shahadarsa, ya kuma tona asirin duk wani mai hannu a cikin wannan badaƙala.
Tags
labari