AMSAR TAMBAYAR DA TSOHON GWAMNAN ZAMFARA YA YI A WURIN TARO A KAN TIRILIYAN DAYA DA YA CE AN BA GWAMNAN ZAMFARA CIKIN SHEKARA 2

Tsohon Gwamnan Zamfara kuma ƙaramin Ministan tsaro na ƙasa Muhammad Bello Matawallen Maradun ya ƙalubalanci gwamna mai ci a taron siyasa da ya gudanar a ranar 13-14 ga Nuwamba,  a Gusau babban birnin jihar. da cewa: "Ko me ya yi da Tiriliyan ɗaya da  ya samu daga gwamnatin tarayya cikin shekara biyu?" Wasu magoya bayan gwamnati mai ci sun amsa tambayar kamar haka:
      1) An biya bashin albashin ma'aikata na wata uku da ka kasa biya har ka bar gwamnati.

       2) An biya bashin kuɗin WAEC da NECO da ka kasa biya shekara 4 lokacin kana gwamna.

    3)  An biya kuɗin ƴan pension daga 2011 zuwa 2025 da gwanatocinku suka kasa biya.

   4) An biya bashin biliyan 316  da ka ciyo ma Zamfara ba tare da ka yi wani aiki ba.

  5) An yi amfani da waɗannan kuɗin wurin sabunta asibitoci da makarantun primary da kuma gina masarautu na zamani a dukkan Ƙananan hukumomi 14 na jihar.

   6) An yi amfani da kuɗin wurin cigaba da gyaran filin sauka da tashin jirage tare da cike giɓin kuɗi biliyan 70 da suka yi ɓatan dabo a gwamnatinka.

  7) Anyi amfani da kuɗin wurin ayyukan raya birane musamman garin Gusau. Wanda kai ka san ba hakanan ka bar garin ba.
  Tiriliyan 1 da kake ikirarin an ba Gwamnan Zamfara cikin shekara biyu kai ka san waɗannan ayyukan kawai da aka zayyano tiriliyan ɗaya ba zata iya yinsu ba.
   
 A Zamfara mun manta da bangar siyasa amma gashi jiya daga shigowarka kana kokarin dawo mana da ita.

    Shin abun tambaya Kai a lokacinka babu Gwamnatin Tarayya ne?

     Shin kai da ka share tsawon shekara 4 akan mulki tiriliyan nawa aka baka?

Shin a tsawon shekara 4 daka shafe kana gwamna kana iya nuna ma Zamfarawa aikin Bilyan 100 da ka yi a duk faɗin jihar Zamfara?

Post a Comment

Previous Post Next Post