Firaministan Senegel Ousmane Sanko ya bayyana juyin mulkin da aka yi a Guiene-Bissau a matsayin abin da bai dace ba.
Mista Sanko ya buƙaci a ci gaba da bayar da damar tattara sakamakon zaɓe domin bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.Yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin ƙasar a birnin Dhakar, Mista Sanko ya ce dole hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.
Tun kafin bayyana zaɓen shugaban ƙasar Omaru Sissico-Embalo ya tsere daga ƙasar, inda ya ce sojoji sun ƙwace mulkin ƙasar.