Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan wasu kalaman da ya yi tare da Sanata Barau Jibrin da gwamnati ke ganin suna da hatsari ga tsaron jihar.
Wannan bukata ta fito ne bayan zaman majalisar zartarwa na mako–mako karo na 34 da aka gudanar a Kano. A cewar gwamnatin jihar, kalaman na su Ganduje da Barau na iya haifar da tsoro a zukatan jama’a tare da kawo tarnaki ga kokarin da ake ci gaba da yi na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa abin takaici ne ganin cewa cikin kasa da sa’o’i 48 bayan fitowar wadannan kalamai, wasu al’umma a jihar sun sake fuskantar harin ’yan bindiga.
Gwamnatin Kano ta kuma gode wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro bisa irin goyon bayan da suke bayarwa wajen tabbatar da tsaro. Ta kara da cewa ba za ta lamunci kafa wata rundunar tsaro ta bogi a cikin jihar ba.
A karshe, gwamnatin ta yi kira ga jami’an gwamnati da ’yan siyasa da su guji yin kalaman da ka iya tayar da hankalin jama’a, tare da tabbatar wa al’ummar Kano cewa tana ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
