Real Madrid Na Dab Da Kulla Yarjejeniya Da Vinicius

Dan wasan Brazil Vinicius Jr na dab da rattaba hannu kan wani sabon kwantaragi da Real Madrid bayan ya rage yawan kudin da yake son a biya shi. Kwantaragin dan wasan mai shekara 25 na yanzu zai zo karshe ne a watan Yunin 2027 (Mundo Deportivo)

Manchester United ta tuntubi wakilan Vinicius Jr, kuma watakila Manchester City ta bi sahunsu idan dan wasan ya yanke shawarar barin kungiyar ta La Liga . (Caught Offside via The Daily Briefing)

Watakila Liverpool ta sayi dan wasan Bournemouth Antoine Semenyo a watan Janairu ko ta jira har zuwa lokacin bazara lokacin da ake sa ran Manchester City za ta shiga kasuwa don siyan dan wasan na Ghana mai shekara 25.(i Paper),

Tsohon kocin Nottingham Forest Ange Postecoglou da kuma tsohon kocin Celtic Brendan Rodgers na cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin kocin Leeds United Daniel Farke wanda ke ci gaba da fuskantar matsin lamba. (Talksport),

Manchester City ta bi sahun Arsenal wajen duba dan wasan Elche dan kasar Sifaniya, Rodrigo Mendoza, mai shekara 20, inda ita ma Real Madrid ke zawarcinsa (Mail, external)

Post a Comment

Previous Post Next Post