Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ya dawo Najeriya cikin jirgin saman Côte d’Ivoire bayan tashin hankalin siyasa da ya faru kwanan nan a Guinea-Bissau, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu ma ya tanadi jirgi domin ɗaukar sa, sai dai Côte d’Ivoire ce ta samu izinin sauka da wuri.
Jonathan, wanda ya je ƙasar ne a matsayin shugaban tawagar sa ido ta West African Elders Forum a zaben ƙasar, ya yi bayani ne a wata hira da ya yi da Symfoni, wadda aka wallafa a YouTube ranar Juma’a wannan shi ne karo na farko da ya yi magana tun bayan harbe-harben da aka ji a kusa da muhimman wuraren gwamnati a Bissau, lamarin da ya tayar da zancen yiwuwar juyin mulki.Ya ce ya ga dacewar yin magana ne domin “jinjina wa ‘yan Najeriya bisa nuna damuwa da addu’o’i” da aka yi masa, yana mai cewa ya san yadda labarin ya tayar wa al’umma hankali.
“A lokacin da muke Bissau kuma aka ce wai juyin mulki ne, bayanan da muka samu sun nuna cewa ƙasa gaba ɗaya ta tada hankula matasa da tsofaffi, ba tare da la’akari da addini ko siyasa ba,” in ji shi.
Jonathan ya bayyana cewa duka shugabannin Najeriya da Côte d’Ivoire wato Shugaba Tinubu da Shugaba Alassane Ouattara sun shirya jirage domin fitar da shi da tawagarsa daga Bissau.
Sai dai, in ji shi, tawagar Côte d’Ivoire ta samu izinin sauka kafin ta Najeriya sakamakon kusanci da ƙasa da kuma alaƙar da ke tsakanin ƙasashen Faransanci da Lusophone.
“Na gode wa ‘yan Najeriya, kuma ina son su ji daga bakina domin nuna godiya bisa damuwar da suka nuna. Na kuma gode wa shugabanmu, Shugaba Tinubu, da Shugaban Côte d’Ivoire, Ouattara.
“Dukkan shugabannin sun shirya jirage domin ɗaukar mu, amma ka san Côte d’Ivoire ce mafi kusa da Guinea-Bissau, sannan akwai kusanci tsakanin ƙasashen Faransanci da na Lusophone. Sun fi samun sauƙi wajen samun izinin sauka kafin Nijeriya ta samu. Shi ya sa jirgin Côte d’Ivoire ya iso da wuri,” in ji Jonathan.
Ya ƙara da cewa lokacin da aka sanar da shi cewa jirgin Najeriya ma ya samu izinin tashin zuwa Bissau, tuni jirgin Côte d’Ivoire ya kusa sauka.
“Da muka ji cewa jirgin Najeriya zai taso, mun ce kada su damu. Shi ya sa a hotunan da kuka gani, jirgin Côte d’Ivoire ne na dawo da ni,” ya bayyana.
A ƙarshe, Jonathan ya gode wa shugabannin ƙasashen biyu da kuma ‘yan Najeriya, matasa da tsofaffi, bisa kulawar da suka nuna a lokacin tashin hankalin.
“Mun gode wa Shugaba Ouattara da Shugaba Tinubu, kuma ina godiya ga ‘yan Najeriya baki ɗaya,” in ji shi.