Tinubu Ne Zai Lashe Zaben Jihar Edo - Gwamna Okpebholo

"Idan Tinubu bai ci jihar Edo a zaɓen 2027 ba to zan sauka daga kujera ta ta gwamna - Okpebholo". Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce a shirye ya yi murabus daga mukaminsa idan Shugaba Bola Tinubu ya gaza lashe jihar a zaben shugaban kasa na 2027.

Gwamna Okpebholo

Gwamnan ya lura cewa jam’iyyar APC yanzu ta mamaye siyasar jihar Edo gaba ɗaya, kuma ba ta fuskantar “wata adawa” a gaban babban zabe mai zuwa.

Yayin da yake magana a wata hira da AIT, Okpebholo ya ce Tinubu na da goyan baya mafi rinjaye a Edo.

Ya bayyana cewa karɓuwar gwamnatinsa da ke ƙaruwa yanzu na da alaƙa kai tsaye da tasirin shugaban kasa a mulkinsa.

“Asiwaju ma ya fi ni farin jini a nan yanzu saboda mutanen Edo sun riga sun fahimci cewa abubuwan da nake yi sakamakon tasirin Asiwaju ne,” in ji gwamnan.

“Za ku ga irin sakamakon da zai fito daga nan saboda babu wasu masu adawa a Edo.”

Post a Comment

Previous Post Next Post