Jam'iyyar hamayyar nan ta African Democratic Congress wato ADC, a Najeriya ta zargi gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC da yankan baya ga fafutukar yaki da matsalar tsaro, ta hanyar yin sulhu da 'yan bindiga a asirce, da biyansu kudin fansa wajen karbo mutanen da aka yi garkuwa da su.
Abin da jam'iyyar ta ADC ke zargin yana mayar da hannun agogo baya wajen magance matsalar ta tsaro, da kuma kara wa 'yan bindigan karfin tattalin arziki.Jam'iyyar dai ta bukaci gwamnatin ta APC da ta fito fili ta yi wa al'ummar kasar cikakken bayani na gaskiya, game da kumbuya-kumbuyar da ake zargin ana yi wajen karbo mutanen da aka yi garkuwa da su.
A wata tattaunawa da BBC daya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta hamayya, Faisal Kabir, ya ce suna murna kamar sauran 'yan Najeriya da sako daliban nan na sakandiren 'yan mata ta garin Maga da ke jihar Kebbi da aka yi, da kuma mutanen da aka sace a jihar Kwara da su ma aka sako su.
Sai dai kakakin ya ce suna jin takaici da yadda matsalar ta tsaro ke kara ta'azzara a kasar, da kuma yadda gwamnati take tafiyar da harkar.
Ya ce: ''Kamar akwai wasu abubuwa da gwamnati take boye wa jama'a wadanda ba ta so su sani.
''Abu na farko shi ne wadannan yaran da aka karbo da kuma mutanen nan, na Kebbi da kuma na Kwaran nan. Shin wadannan mutanen karbo su aka yi daga wajen 'yanbindigan nan ko kuma a'a fada aka yi aka kwato su? Domin a cikin wasu bayanai da shugaban 'yansanda ya fitar ya nuna cewa kamar wadannan 'yanbindiga saranda suka yi suka sako mutanen.
''Kuma bayanin da Bayo Onanuga ma ya yi mai magana da yawun shugaban kasa yana nuna cewa kamar su wadannan mutanen wadanda suke shiga tsakani sun fada musu maganganu masu dadi shi ne ya sa suka sako wadannan yaran.
'To idan dai ko haka ne wannan gwamnati tana da hanya da za ta tattauna da 'yanbindiga domin ta smau hanya mafi sauki wadda za ta kwato wadannan yara maimakon ko murkushe su ne ta yi gabadaya, to lalle tabbas kuwa kasar nan tana cikin hadari.''
Kakakin na ADC, ya ara da cewa: ''Zai yi wahala a ce tattaunawar da aka yi da su ba kudi aka ba su ba, in kuwa kudi aka ba su to ka ga an kara musu karfin tattalin arziki da za su kara siyan makamai. Idan kuwa yakarsu aka yi to ya kamata a gaya mana mutum nawa aka kashe ko kuma a nuna mana bidiyon yadda abubuwan suka faru.''
A martanin da daya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyar ya yi kan zarge-zargen na ADC, Daniel Bwala, ya ce maganganu ne kawai irin na mai kaikayin baki kawai irin na wadanda ba sa ganin abu sai sun tanka.
Ya ce, wanda duk yake sauraron irin abin da suke faruwa a Najeriya kuma yana duba irin abubuwan da suke zai gan cewa wannan matsala ce da take da girma sosai fiye da abin da mutane suke tunani.
''Maganar cewa muna ba wa mutanen bandit kudi ko ba ma ba su kudi, bayanan a fili suke, kuma abin da gwamnati ta fada kan yadda ake ceto yaran daga hannun mutanen bandit din an fada,'' in ji Bwala.
Kakakin na Tinubu ya kara da cewa: ''Komai da gwamnati ya kamata ta yi ta tabbatar cewa mutane suna cikin kwanciyar hankali ko kuma wadanda aka kama a karbo su shi ne aikin da gwamnati ta yi.''
Yanzu dai fata 'yan Najeria a kan wannan kalubale na tsaro da ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na kasar, musamman yankin arewacin kasar shi ne su ga lokacin da za a kai ga dakile ta.