Rahotonni daga birnin Ibadan na jihar Oyo na cewa gwamnonin jihohin Osun da Taraba da kuma Rivers ba su halarci babban taron jam'iyyar PDP da ke guda a birnin ba.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa ba a ga fuskokin gwamnonin a wurin taron ba.Babbar jam'iyyar hamayyar ta Najeriya na gudanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabbin shugabanninta.
An dai samu mabambantan umarnin kotuna da suka ci karo da juna game da taron, inda wasu suka bai wa jam'iyyar damar ci gaba da taron, yayin da wasu kuma suka hana.
Jam'iyyar ƙarƙashin tsagin shugabanta na ƙasa, Amb. Iliya Damagum ta ci gaba da gudanar da taronta a birnin na Ibadan.
Kawo yanzu gwamnonin da suka hallara a wurin taron sun haɗar da na jihohin Bauchi da Plateau da Zamfara da kuma Oyo mai masaukin baƙi.
Haka kuma akwai tsoffin gwamnonin jihohin Akwa Ibom da Neja da kuma Kano.