Masana’antar Kiwo Da Fitar Da Jata Ta India na Fuskantar Barazana Duk Da Ita Ce Ta Biyu Mafi Girma A Duniya

 Ƙasar India, wacce ita ce ta biyu mafi girma wajen samar da jata (shrimp) a duniya, tana fuskantar babban ƙalubalen da ka iya jefa masana’antarta cikin rikici.

Jata

Masana sun bayyana cewa masana’antar jatan ƙasar, wacce take da darajar biliyoyin daloli, na fama da matsaloli da suka haɗa da yaduwar cututtuka a gonakin ruwa, tsadar kayan aiki, da kuma faɗuwar farashin jata a kasuwannin duniya.

Wadannan matsalolin sun jefa manoma musamman a Andhra Pradesh, Tamil Nadu, da Odisha cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi, inda yawancin jama’a ke dogaro da kiwon jata don samun abin rayuwa.

Masana harkar sun gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakai cikin gaggawa ba wajen ƙawance cututtukan da ke addabar jatan da kuma ba da tallafin kuɗi ga manoma, masana’antar na iya fuskantar mummunar koma baya.

A halin yanzu, India na fitar da mafi yawan jatanta zuwa Amurka, China, da ƙasashen Turai, amma raunin tattalin arzikin duniya da hauhawar farashi sun rage bukatar kayan daga wajen.

Masana tattalin arziki sun ce idan gwamnati ba ta yi gaggawar ɗaukar matakan tallafi ba, masana’antar jatan India na iya durƙushewa, abin da zai shafi dubban jama’a da ke dogaro da ita wajen rayuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post