Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar hare-hare da taɓarɓarewar tsaro a arewacin Najeriya na haifar da yunwa a matakin da ba a taɓa gani ba.
Bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa kusan mutane miliyan 35 za su fuskanci rashin abinci mai tsanani a lokacin fari na 2026, mafi girma da aka taba samu a Najeriya kuma mafi girma a nahiyar Afirka baki ɗaya.Bayanan shirin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa, ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun tsananta kai hare-harensu a wannan shekara ta 2025.
A watan da ya gabata kaɗai, an ruwaito cewa, ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda ke da alaƙa da al-Qaeda, ta kai hare-harenta na farko a Najeriya.
A lokaci guda, ita ma ƙungiyar ISWAP na faɗaɗa tasirinta a arewacin Najeriyar da yankin Sahel.
Daga cikin hare-haren da ƙungiyoyin suka kai a baya-bayan nan, sun haɗa da kwanton-ɓaunar da suka yi wa dakarun sojin Najeriya a jihar Borno, har ma suka halaka wani janar, da waɗanda aka kai makarantu har ma aka sace ɗaruruwan ɗalibai.
''Masu ɗauke da makamai sun zama babbar barazana ga zaman lafiya a Najeriya, kuma illolinsu na wuce iyakokin kasar," in ji David Stevenson, Daraktan shirin a Najeriya.
Ya ƙara da cewa: ''Jama'a na fuskantar matsin lamba daga hare-haren da ake kaiwa abin da ke haifar da yunwa, domin a yankuna da dama fargaba na hana manoma zuwa gona don noma abinci, ga shi kuma buƙata na karuwa''.
Shirin ya ƙara da cewa al'ummar arewacin ƙasar ne suka fi fuskantar tasirin rashin tsaron daga shekaru goma zuwa yanzu, inda manoma a karkara ba sa iya zuwa gonakinsu.
Ya ƙara da cewa kusan mutane miliyan shida ne ke fama da rashin abinci a yankunan da rikici ya shafa a jihohin Borno, da Adamawa, da Yobe.
Hasashen ya nuna cewa mutum kimanin dubu goma sha biyar a Borno kaɗai za su gamu da matsananciyar yunwa ta innanaha, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don ceton rayuwarsu.
A gefe guda kuma dama tuni yara na cikin wani mummunan yanayi na fama da tamowa a musamman a Sokoto, da Katsina da Yobe, da Zamfara, inda rashin abinci mai gina jiki ya fi yawa.
A yanzu dai kusan mutane miliyan ɗaya ne ke dogaro da taimakon abinci daga Majalisar Ɗinkin Duniya.
Kuma suk da haka, ƙarancin kuɗaɗe ya tilasta wa hukumar rage wasu shirye-shiryen a watan Yuli, wanda ya shafi yara sama da 300,000.
A wuraren da asibitoci suka daina aiki kuwa, rahoton na WFP ya ce matsalar rashin abinci mai gina jiki ta taɓarɓare daga mataki ma "mai tsanani" zuwa mataki "mai matuƙar haɗari" a zango na uku na wannan shekara.