KO NAJERIYA NA BUKATAR KARIN YANSANDA DON TUNKARAR MATSALAR TSARO?

Masana al'amuran tsaro da ƴan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan sanarwar da Shugaban Ƙasar Bola Tinubu ya fitar na ɗaukar sabbin jami'an ƴansanda a ƙasar.

A ranar Lahadi ne Shugaba Tinubu ya umarnci babban sifeton ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun cewa rundunar ƴansandan ƙasat ta ɗauki sabbin jami'ai 30,000 domin ƙarfafa samar da tsaron a faɗin ƙasar.

Matakin shugaban ƙasar na zuwa ne bayan sace ɗaruruwan ɗalibai wasu makarantun Kebbi da Neja cikin makon da ya gabata.

''Matakin zai taimaka wajen bunƙasa wanzuwar jami'an ƴansanda a duka garuruwan ƙasar nan'', in ji Tinubu.

A cikin 'yan shekarun nan batun ƙarancin yawan 'yansanda a Najeriya na daga cikin abubuwan da ake kallo ya na janyo matsala wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.

Ana ƙiyasta cewa yawan adadin ƴansandan Najeriya ya kai fiye da 350,000.

A shekara 2022, hukumar ƙididdiga ta ƙasar NBS, ta yi ƙiyasin cewa adadin jami'an ƴansandan Najeriya sun kai aƙalla 250,276.

To amma a wani ƙiyasi da hukumar kula da masu neman mafaka ta tarayyar Turai, (European Union Agency for Asylum) ta yi a 2025, ya nuna cewa adadin jami'an ƴansandan Najeriya ya kai 371,800.

Akwai ƙiyasin Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna cewa ana buƙatar kowane mutum 600 a samu jami'in ɗansanda daya da zai kula da su.

To amma Dokta Kabiru Adamu ya ce binciken kamfaninsa da tuntuɓar MDD bai tabbatar da wannan iƙirari ba.

Maimakon haka ya ce adadin ƴansandan da kowane ƙasa ke buƙata ya danganta da irin buƙatun matsalolin tsaronta.

''A kimiyanve babu wata ƙa'ida da aka tsayar na adadin mutanen da kowane ɗansanda zai kare'', in ji Dokta Kabiru Adamu.

To amma masanin tsaron ya ce akwai abubuwa da ake la'akari da su wajen adadin jami'an da ake so.

''Akwai jami'in da za ka yi masa horo ya kuma yi maka aiki irin na jami'ai 10, haka kuma akwai wanda sai ka ɗauki jami'ai 10 sannan su yi maka aikin jami'i guda, ya danganta da irin horon da jami'an suka samu'', in ji shi.

Haka kuma ya ƙara da cewa ana la'akari da irin kayan aikin da jami'an za su yi amfani da su, kamar na'urorin fasaha irin kyamarorin tsaro.

''Akwai kyamarar tsaro da za ka saka ta yi maka aikin jami'ai 100, abin da kawai kake buƙata wataƙila shi ne saka jami'ai biyu a ɗaki domin lura da na'urar'', in ji shi.

Masanin tsaron ya ci gaba da cewa aikin ɗansanda na da nau'ika masu yawa.

''Hukumar Nigerian Police Force ba ita kaɗai ba ce ke gudanar da ayyukan da ya kamata ƴansanda su yi a ƙasar'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa akwai sauran nau'ikan hukumomin tsaro masu yawa da ke aiki irin na ƴansanda a Najeriya.

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai hukumomin tsaro a Najeriya har wajen takwas da aikin ƴansanda suke yi.

''Alal misali hukumar shige da fice ta Najeriya da hukumar EFCC da ICPC masu yaƙi da cin hanci da rashawa duka aikin da suke yi na ƴansanda ne'', in shi ji.

Dokta Kabiru Adamu ya ce a duk lokacin da ake magana kan jami'an ƴansandan Najeriya, ya kamata a rika la'akari da waɗannan.

''Don haka bai kamata kai-tsaye a ce akwai ƙarancin ƴansanda a Najeriya, saboda akwai takwarorinsu jami'an tsaro da ke irin aikinsu'', in ji shi.

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin sabunta wuraren bayar da horo ga jami'an ƴansanda da ke jihohin ƙasar.

To amma wani tsohon jami'in ɗansanda, SP Habibu Shehu Yakawada mai murabus ya ce adadin ƴansandan da Najeriya ke da su a yanzu sun gaza.

''Yanzu haka adadin ƴansandan ƙasar bai kai 500,000 ba kuma ta ina wannan adadin zai wadatar da Najeriya, da ke da jihohin 37 haɗe da babban birnin kasar Abuja'', in ji SP Yakawada mai murabus.

Har ila yau SP Yakawada mai murabus, ya ce akwai buƙatar gwamanti Najeriya ta yi wa ƴansadan ƙarin albashi don zaburar da su ƙara himma wajen kawar da ta ɓata gari a tsakanin al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post