RSF Da Gwamnatin Sudan Sun Yi Watsi Da Tayin Trump Na Tsagaita Yaki - Amurka

Babban mai ba Shugaban Amurka Donald Trump shawara akan Afirka ya ce dakarun sojin Sudan da na 'yan tawayen RSF sun yi watsi da tayin da Amurka ta yi musu na neman a tsagaita wuta.

Massad Boulos ya ce ya ce ya saurari bangarorin biyu bayan da aka bayar da sanarwar tsagaita wutar a jiya Litinin tare da cewa ya zama wajibi su kawo karshen yakin basasar da ya dauki lokaci ana yi ba tare da gindaya kowane sharadi ba na dole ba.

Rundunar sojin Sudan din ta yi watsi da wani daftarin dakatar da buɗe wutar da ke samun goyon bayan asasr Hadaddiyar Daular Larabawa, tana mai cewa yarjejeniyar ta fifita RSF.

Yarjeniyoyin dakatar da buɗe wuta da aka rika yi a baya - sun rika rushewa, tun ba a je ko'ina ba. Dubban fararen hula aka kashe tun da yaƙin basasar ya ɓarke a 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post