Yadda Mike Tyson Ya Sauya Sheka Zuwa Addinin Muslunci

Tsohon zakaran damben duniya ajin masu nauyi "Mike Tyson" ya musulunta a lokacin da yake daure a shekarun 1990s, ya kasance musulmi har zuwa yau. Tyson ya sha yin magana game da tafiyarsa ta addini zuwa Makkah, yana mai cewa, "Na yi matukar farin ciki da zama musulmi. Allah ba ya bukatata, nine nake bukatar Allah". Ya kuma ce, "Ni Musulmi ne, amma ina girmama dukkan addinai ... Ina yawan yin salla, kuma zan mutu, ina so in mutu a matsayin musulmi". 

Mike Tyson

Tyson ya karbi Musulunci yayin da yake zaman gidan yari tsakanin 1992 zuwa 1995, daya musulunta ya sami nutsuwa a lokacin tashin hankali a rayuwarsa. Bayan musuluntarsa ya mayar da sunansa Malik Abdul Aziz.

Ya yaba wa Musulunci da samar masa da alkibla na ɗabi'a, da tushen ruhi, da kuma taimaka masa ya zama mai rikon amana, musamman a cikin rayuwar iyalinsa.

Yayin da yake bayyana shi a matsayin musulmi mai kishin addini, ya yi aikin hajji a Makka a shekarar 2022. Mutane da yawa suna ganin lamarinsa a matsayin misali mai ƙarfi na ikon canza bangaskiya da ci gaban dan adam.

Post a Comment

Previous Post Next Post