Ko An Biya Kudin Fansa Kafin Sakin Daliban Kebbi?

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya ce ɗaliban jihar da aka kuɓutar daga hannun ƴanbindiga na cikin ƙoshin lafiya.

A wani taron manema labarai da gwamnan ya gabatar a fadar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi jim kaɗan bayan sanar da sakin ɗaliban, gwamnan ya gode wa shugaba Tinubu da sauran jami'an tsaro da suka taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban.

''Daga bayanan da muke da su yanzu haka yaran suna kan hanya, kuma suna cikin ƙoshin lafiya, lafiyar kalau aka same su'', in ji shi.

Gwamna Nasir Idris ya kuma ce ba a biya ko sisin kwabo ba a matsayin kuɗin fansa, domin karɓo ɗaliban 24.

''Mun bincika koda an biya kuɗin fansa ne, kuma daga bayanan da muka samu ba a biya kuɗin fansa ba, mu dai gwamnatin jihar Kebbi ba mu biya ko kwabo ba, kuma su ma jami'an da suke je karɓo su sun ce ba su je da kuɗi ba'', in ji shi.

Gwamnan ya kuma gobe za a damƙa ɗaliban a hannun iyayensu.

A makon da ya gabata ne aka sace ɗaliban a makarantar sakandiren ƴanmata da ke Maga a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post