Abubuwa Hudu Dake Kai Mutane kasar India

1. Neman lafiya: India ƙasa ce wacce ta yi fice a fagen ilimin kiwon lafiya, tiyata da jinya.

Jirgi

- India tana da ƙwararrun likitocin tiyatar zuciya, ƙoda, tiyatar cutar kansa, tiyatar ƙashi da magunguna

- India tana da sauƙin farashin magani ingantacce kuma mai rahusa

- India tana da na'urorin tiyata irin na zamani (high-tech medical equipment)

2. Neman ilimi: India ƙasa ce da tayi fice wurin inganta ilimin kiwon lafiya, kimiyya da fasaha musamman (Medicine, Engineering da Computer Science)

Duk ɗalibin da ya samu ingantaccen ilimi daga ƙasar india, to babu shakka zai amfani duniya watarana.

3. Tsafi da sihiri: India ƙasa ce wacce ta yi fice a gurin aikata mummunan sihiri da baƙin tsafi (Tantirik da black magic) 

4.  India ƙasa ce da ta yi fice gurin siyar da kayan wutar lantarki ingantattu "Electronics" da kayan sawa na tufafi "Textiles" da kuma sinadaran Chemicals da kamfanoni ke amfani da su. Daga shafin Fezbuk na Alhassan Mailafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post