yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a wasu sassan Arewa maso Yamma, al’ummar Zariya sun shiga fargaba a ranar Talata bayan da wata ƙaramar jaka ɗauke da harsashi ta faɗo daga wata mota da ke wucewa.
Wani gajeren bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jama’a suka yi cunkoso a gefen hanya suna duban jakar da kuma ɗimbin harsashin da ya warwatsu a ƙasa. Mutanen cikin motar ba su tsaya ba bayan jakar ta faɗi, lamarin da ya haifar da ruɗani ko dai ba su lura da abin da ya faru ba ko kuma sun ƙi tsayawa saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.Lamarin ya ƙara damuwar jama’a, musamman ganin cewa al’ummomin yankin na ci gaba da fama da hare-haren ’yan bindiga da barazanar tsaro iri-iri. Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ba tukuna, amma masana tsaro na cewa wannan al’amari ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da asali da kuma inda aka nufa kai wannan makamai.
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi tare da kwantar wa jama’a hankali a damuwa game da yaduwar makamai a yankin.