Masu garkuwa da mutane, da satar dabbobi, sun sake fasa Kano.
A jiya Talata 25/11/2025, ɓarayin daji sun sake ƙuƙutawa sun shiga wani yanki na jihar Kano da yake iyaka da jihar Katsina, inda suka shiga ƙauyuka guda uku suka yi awon gaba da mutane maza da mata a ƙauyukan: Sundu da Birisawa da kuma Masaurari dukkansu a ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.
An saurari jami'in hulɗa da jama'a na Kano Abdullahi Haruna kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar abin, ya kuma shaida wa manema labarai cewa, har yanzu ana cikin neman waɗannan mutane tare da gurfanar da 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da su.
Wannan labari ya fito ne jim kaɗan bayan da aka samu labarin an sako ɗaliban makaranta 24, da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi Nijeriya.
Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifa.
Me za ku ce game da wannan yawan hare-haren da yake ƙaruwa a yankunan jihar Kano a cikin 'yan kwanakin nan?