Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa jami'an tsaro umurnin su yi wa dajin jihar Kwara ƙawanya, sakamakon ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a yankin.
Shugaban ƙasar ya kuma umurci sojojin sama su faɗaɗa ayyukansu na sa ido har zuwa tsakiyar dazukan inda ake tunanin ƴan ta'addan na ɓoya.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan sadarwa, Sunday Dare ya fitar, ya kuma ce shugaban ya bayar da umurnin yin hakan a yankunan Kebbi da Neja, inda ake sa ran ceto yara a Neja.
Ya kuma ce wajibi ne sojojin sama su riƙa aikin sa ido awa 24 domin taimaka wa aikin da sojojin ƙasa ke yi.