Za a Kafa Cibiyoyin ICT Touchpoint a Kananan Hukumomi 34 Dake Jihar Katsina

Gwamna Radda ya Kaddamar da Layin Sadarwar Fibre Metropolitan Area Network Da Kuma Tsarin Samar da Wutar Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana Mai Zaman Kansa Don Sauya Fasahar Zamani a Katsina.

Dikko Umar Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda Phd. CON, ya kaddamar da sabuwar hanyar sadarwar Zamani (Katsina Metropolitan Area Fibre Network) tare da Tsarin Samar da Wutar lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana mai zaman kansa, inda ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin manyan nasarori da za su hanzarta karɓar fasaha, fadada damar intanet, tare da samar da sabbin damar tattalin arziki ga matasan jihar.

An gudanar da kaddamarwar ne yau a cibiyar KATDICT,  jim kadan bayan kammala taron (Invest Katsina Economic Summit) wanda ya kasance daya daga cikin gagarumin matakan gwamnatin wajen karfafa ginin tsarin sadarwar zamani da sanya Jihar Katsina a sahun gaba wajen bunƙasa kirkire-kirkiren fasaha. Gwamna Radda ya jaddada cewa wannan kaddamarwar wani muhimmin mataki ne na digitizing da sabunta tsarin mulki, yana mai cewa “Dijital ita ce hanyar gaba, kuma Katsina ba za ta tsaya a baya ba.”

Gwamnan ya bayyana cewa wannan aiki ya samu ne sakamakon muhimmiyar manufar gwamnati – soke kudaden Right of Way (RoW) – wanda ya ja hankalin zuba jari sama da Naira biliyan 4 wajen shimfiɗa kebul ɗin fibre-optic har tsawon kilomita 25 a cikin birnin Katsina.

Ya ce wannan layin sadarwa zai fadada damar samun intanet mai sauri da inganci, wanda zai bai wa matasa maza da mata damar amfani da fasaha wajen ilimi, kasuwanci, aikin nesa (remote work), da cikakken shiga duniyar dijital. Ya nuna cewa tattalin arzikin duniya yanzu yana karkata ne zuwa fasahar bayanai, don haka wajibi ne matasan Katsina su samu kayan aiki da damar gogayya da takwarorinsu.

Gwamna Radda ya kara da cewa layin fibre shi ne ginshiki na ganin an cimma burin “One Government Enterprise”, inda dukkan ayyukan gwamnati za su kasance dijital kuma na atomatik, kana al’umma za su rika samun hidimomin gwamnati daga na’urorinsu da dannawa daya kacal.

Ya jaddada cewa yankin Arewa ta Najeriya ya dade yana baya wajen karɓar fasahar zamani, don haka akwai bukatar matakin gaggawa da gwamnati za ta dauka domin budewa matasa manyan damar ci gaba a duniyar dijital.

Gwamnan ya yaba wa abokan aikinsa IHS bisa hadin kai, tare da tabbatar da cewa gwamnati a shirye take ta karɓi dukkan kamfanonin da ke aikin ICT. Ya bayyana shirin tabbatar da cewa dukkan hedikwatar kananan hukumomi za su samu intanet kyauta, daya daga cikin muhimman manufofin sauya tsarin dijital na Jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post