Ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru, ya ce ma'aikatarsa na bincke a kan jayayyar da aka samu tsakanin ministan birnin tarayyar ƙasar, Abuja Nyesom Wike da kuma wani hafsan sojin ruwa, A. M. Yerima a kan dambarwar ikon mallakar fili.
A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Badaru ya ce rundunar sojin Najeriya ba za ta taɓa juya baya ga duk wani jami'inta da ke gudanar da aikinsa a kan doka ba.Badaru ya sanar da hakan ne bayan jayayyar da aka yi tsakanin Nyesom Wike da jami'in sojin ruwa, A.M Yerima a ranar Talata 11 ga watan Nuwamba, lamarin da ke ci gaba da jan hankalin jama'a a ƙasar.
Ministan ya ce "A matsayin ma'aikata da kuma rundunar sojin Najeriya, za mu kasance masu bayar da kariya ga duk wani jami'inmu da ke kan ƙa'idar aikinsa.
"Muna nazari kan batun, kuma muna bayar da tabbacin cewa za mu kare duk wani jami'inmu da ke kan aikinsa bisa doka. Ba za mu taɓa bari wani abu ya faru da jami'inmu da kje gudanar da aikinsa yadda doka ta yi tanadi ba.''
A ranar Talata bidiyon jayayya tsakanin ministan birnin Abuja da wani matashin hafsan sojin ruwa ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ministan ya yi jayayya da sojan a kan wani fili da ake ginawa mallakin tsohon babban hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo.
Wike da tawagrasa sun ziyarci wajen da filin yake tare da neman a nuna masu takardun izinin mallakar filin.
Ministan ya haƙiƙance cewa ba a cika ƙa'ida ba wajen mallakar takardun filin.
Sojojin kuma sun hana ministan shiga filin, lamarin da ya fusata shi har ta kai ga musayar kalamai.