Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen mutane 32 da ya zaba a matsayin jakadu zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa.
A cewar wata sanarwa da Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Bayani da Tsara Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, jerin sunayen sun haɗa da jakadu 17 na siyasa da jakadu 15 na ƙwararru, waɗanda za a tura zuwa ƙasashe da kungiyoyin duniya masu muhimmanci ga harkokin diflomasiyyar Najeriya.Sunayen da suka fito fili sun haɗa da:
-
Barrister Ogbonnaya Kalu (Abia)
-
Reno Omokri (Delta) – Tsohon hadimin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan
-
Farfesa Mahmood Yakubu (Bauchi) – Tsohon Shugaban INEC
-
Erelu Bisi Angela Adebayo (Ekiti) – Tsohuwar Matar Gwamnan Ekiti
-
Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) – Tsohon Gwamnan Jihar Enugu
-
Tasiu Musa Maigari (Katsina) – Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Katsina
-
Yakubu N. Gambo (Plateau) – Tsohon Kwamishina, kuma tsohon Mataimakin Sakataren Hukumar UBEC
-
Farfesa Nora Ladi Daduut (Plateau) – Tsohuwar Sanata
-
Otunba Femi Pedro (Lagos) – Tsohon Mataimakin Gwamna
-
Chief Femi Fani-Kayode (Osun) – Tsohon Ministan Sufuri
-
Barr. Nkechi Linda Ufochukwu (Anambra) – Lauya
-
Fatima Florence Ajimobi (Oyo) – Tsohuwar Matar Gwamnan Oyo
-
Lola Akande (Lagos) – Tsohuwar Kwamishina
-
Grace Bent (Adamawa) – Tsohuwar Sanata
-
Dr. Victor Okezie Ikpeazu (Abia) – Tsohon Gwamnan Abia
-
Sanata Jimoh Ibrahim (Ondo) – Dan kasuwa, tsohon Sanata
-
Ambassador Paul Oga Adikwu (Benue) – Tsohon Jakadan Vatican
-
Enebechi Monica Okwuchukwu (Abia)
-
Yakubu Nyaku Danladi (Taraba)
-
Miamuna Ibrahim Besto (Adamawa)
-
Musa Musa Abubakar (Kebbi)
-
Syndoph Paebi Endoni (Bayelsa)
-
Chima Geoffrey Lioma David (Ebonyi)
-
Mopelola Adeola-Ibrahim (Ogun)
-
Abimbola Samuel Reuben (Ondo)
-
Yvonne Ehinosen Odumah (Edo)
-
Hamza Mohammed Salau (Niger)
Jakadu masu ƙwarewa sun haɗa da:
Ambassador Shehu Barde (Katsina), Ambassador Ahmed Mohammed Monguno (Borno), Ambassador Muhammad Saidu Dahiru (Kaduna), Ambassador Olatunji Ahmed Sulu Gambari (Kwara), Ambassador Wahab Adekola Akande (Osun).
Ana sa ran za a tura su zuwa muhimman ƙasashe irin su China, India, South Korea, Canada, Mexico, UAE, Qatar, South Africa, da Kenya, tare da wuraren aikace-aikace na din-din-din kamar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), UNESCO da Tarayyar Afirka (AU).
Za a bayyana wuraren da za su tafi aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance su ta kuma amince da nadin nasu.