Rundunar Sojojin Najeriya ta kara wa jami’ai 28 masu mukamin Brigadier General girma zuwa Major General, tare da karin Colonels 77 zuwa mukamin Brigadier General, a wani muhimmin sauyin jagoranci da ya shafi manyan hafsoshin rundunar.
Wannan sanarwa ta fito ne daga Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soja, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta shafin X na Rundunar Soja a ranar Juma’a.Daga cikin waɗanda aka haɓaka zuwa Major General akwai:
-
Brig Gen O. Adegbe na Defence Intelligence Agency
-
Brig Gen S. M. Uba, Daraktan Defence Information
-
Brig Gen R. E. Hedima, Acting Chief of Military Intelligence (Army)
-
Brig Gen R. T. Utsaha, Mataimakin Daraktan Defence Operations
Sauran sun haɗa da:
-
Brig Gen A. M. Umar, Commandant na Warrant Officer Academy
-
Brig Gen S. Sulaiman, Deputy Military Secretary (Army)
-
Brig Gen I. O. Bassey, Daraktan Army Operations Centre
-
Brig Gen C. A. Ekeator na Nigerian Army School of Electrical and Mechanical Engineering
Haka kuma an haɓaka:
-
Brig Gen S. Y. Yakasai, Acting Director Procurement a Ofishin COS
-
Brig Gen W. L. Nzidee, Sashen Army Logistics
-
Brig Gen S. A. Emmanuel na sashen Signals
-
Brig Gen S. S. Tilawan, Acting Commander Sector 3, Operation HADIN KAI
-
Brig Gen M. O. Agi, Desk Officer na TETFund a NDA
-
Brig Gen I. M. Abbas, Commander 34 Brigade
Haka kuma, Brig Gen Z. A. Saidu ya samu haɓakawa posthumous a girmamawa ga hidimarsa ga ƙasa.
A jawabinsa, Babban Hafsan Sojin Najeriya (COAS), Lt Gen Waidi Shaibu, ya taya jami’an da iyalansu murna, yana mai jaddada cewa ƙarin girman ya zama ƙarin dalili na ƙwarewa, ƙwazo da ƙarin jajircewa wajen gudanar da aiki.
Ya buƙace su su zama shugabanni na koyi, su inganta halayensu na aiki, su kuma rungumi sabbin dabarun zamani wajen magance ƙalubalen tsaron da ke ƙara rikitar da ƙasar.
Shaibu ya kuma jaddada muhimmancin riƙon amana, bin doka da kundin tsarin mulki, da kuma cikakken biyayya ga Najeriya a duk lokacin da ake buƙata.
Wannan ƙarin girma, in ji rundunar, wani mataki ne na ƙarfafa sahun manyan hafsoshi don inganta ayyukan runduna da ƙara karfin martani ga barazanar tsaro a fadin ƙasa.