Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kuɓutar da wasu ƴanmata 12 da mayaƙan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke yankin ƙaramar hukumar Askira/Uba da ke jihar Borno.
Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar da yammacin ranar Asabar, sun ce yanzu haka ƴanmatan na wani sansanin soji mai tsaro domin kula da lafiyarsu, kafin sada su da iyalansu.An dai sace ƴanmatan ne ranar 23 ga watan Nuwamba, lokacin da suke tsaka da aiki a wata gona a jihar Borno, inda mayaƙan ISWAP ke gudanar da harkokinsu.
Rundunar sojin ta kuma yaba wa dakarunta da sauran haɗin guiwar jami'an tsaron da suka taimaka wajen kuɓutar da ƴanmatan
Sanarwar dai ba ta yi cikakken bayanin yadda aka ceto su ba.