Venezuela ta yi Allah Wadai Da Barazanar Mulkin Mallaka Da Trump Ya Yi Musu

Ƙasar Venezuela ta yi Allah wadai da abin da ta kira da barazanar mulkin mallaka da ta ce shugaban Amurka na yunƙurin yi mata.

A ranar Asabar ne Shugaba Trump ya yi barazanar rufe sararin samaniyar ƙasar domin yaƙar abin da ya kira masu safarar ƙwayoyi.

To amma cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Venezuelan ta fitar, ta ce Amurka ba ta ikon rufe sararin samaniyar wata ƙasa, don haka wannan mataki ya saɓa wa ƙa'ida.

Wani ɗan majalisar dattawan Dimokrats a Amurka ya ce irin wannan mataki da gwamnatin Trump ke ɗauka da ya bayyana da na rashin tunani na jefa ƙasar cikin shiga wani fage irin na yaƙi da wata ƙasa.

A nata ɓangare gwamnatin Amurka ta ce tana ɗaukar matakin ne da nufin lalata hanyoyin safarar ƙwayoyi.

To sai dai Venezuela ta ce manufar Amurkan shi ne hamɓarar da gwamnatin Shugaba Nicolás Maduro.

Post a Comment

Previous Post Next Post