Tsohon Firayim Ministan Koriya Ta Kudu Da Shugaban Leken Asiri Sun Shiga Hannu Bisa Zargin Ayyana Dokar Soja

 Hukumomin Koriya ta Kudu sun kama tsohon Firayim Minista tare da tsohon shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar, bisa zargin cewa suna da hannu a yunƙurin ayyana dokar soja a ƙasar.

Hukumomin Koriya ta Kudu

Rahotanni sun bayyana cewa, an cafke mutanen ne bayan hukumar bincike ta musamman ta gano cewa sun taka rawa wajen tsara shirin da zai ba sojoji damar karɓar iko a lokacin da ake cikin rikicin siyasa a kasar.

Masu bincike sun ce shirin dokar soja din an kulla shi ne a lokacin da ake fuskantar zanga-zangar neman sauke shugabar kasa Park Geun-hye daga mulki a shekarar 2017, amma bai samu nasarar aiwatarwa ba.

Wadanda ake zargin, ciki har da tsohon Firayim Ministan, sun musanta laifin, suna mai cewa shirin bai wuce “matakin tsaro na wucin gadi” ba, domin kare zaman lafiya a kasar.

Masu sharhi sun bayyana cewa wannan kama wani babban ci gaba ne wajen tabbatar da gaskiya da adalci a Koriya ta Kudu, inda aka sha kama manyan jami’an gwamnati bayan kammala mulkinsu.

An dai ce za a gurfanar da su a kotu cikin makonni masu zuwa domin fuskantar shari’a.

Post a Comment

Previous Post Next Post