Yadda Aka Kashe Halifan Musulunci Sayyadina Umar Bn Al-Khattab

A ƙarshen shekara ta Ashirin da uku bayan hijira ne Sayyidina Umar (RA) ya yi mafarkin wani jan zakara ya saƙƙwace shi sau biyu. Da ya labarta ma Asma'u ɗiyar Umais (matar da Ali ya aura bayan ta yi wa Abubakar wankan takaba) wadda an san ta da fassarar mafarki, sai ta ce masa, wani Ba'ajame zai kashe ka.

Balarabe

A tsarin gwamnatin Umar (RA) duk namijin da ya balaga daga cikin kafirai ba a ba shi damar zuwa Madina. Amma Mughirah ɗan Shu'ubah, Gwamnansa na Kufa ya nemi izninsa domin ya turo masa wani yaro mai hazaƙa daga cikin 'ya'yan farisa ana kiransa Abu Lu’lu’ata wanda kuma bai musulunta ba. Yaron ya ƙware wajen sana'oin hannu kamar ƙira da sassaƙa da zane da makamantansu. Sayyidina Umar (RA) ya ba da izni.

Bayan da Abu Lu’lu’ata ya tare a Madina, ya nemi sassaucin harajin da Mughirah ya ɗora masa a wajen Sarkin Musulmi Umar. Umar ya tambaye shi nawa kake biya a shekara? Ya ce, Dirhami ɗari. Umar ya ce, mene ne sana'arka? Ya ce, ƙira da sassaƙa da zane. Sai Umar ya ce, to in haka ne ai Dirhami ɗari ba su yi ma yawa ba.

A daidai lokacin da Sarkin Musulmi ya ba da umurnin a rage ma Abu Lu’lu’ata haraji, shi kuma yana can yana shirin ganin bayansa.

A safiyar 26 ga watan Dhul Hajji 23 bayan hijira wanda ya yi daidai da 3 Ga Watan Nuwamba 644, Sarkin Musulmi Umar ya fito zuwa Masallaci kamar yadda ya saba, ba tare da ɗan rakiya ko wani jami'in tsaro ba. Da aka fara Sallah Umar ya shiga gaba, ya daidaita sahun mutane Sannan ya fara Sallah. Gama Fatiharsa ke da wuya sai aka ji tsit, waɗanda suke wajen Masallaci ba su san abin da ke gudana ba. Can kuma sai aka ji muryar Abdur Rahman ɗan Aufu yana ci gaba da Sallah, kuma ya taƙaita ta sosai.

Daga cikin Masallaci kuwa, waɗanda ke kusa sun shedi Abu Lu’lu’ata ya kutsa a tsakanin mutane yana sukarsu da wuƙa, sai da ya soki mutane 13 kafin ya kai zuwa ga liman, ya kuma yi masa suka shida a wurare daban – daban cikinsu har da wata guda ɗaya a kuiɓinsa. Sayyadina (RA) bai kai ƙasa ba sai da ya janyo Abdur Rahman ɗan Aufu ya sanya shi a matsayinsa don ya ci gaba da ba da Sallah ga mutane. Bamajushe ya yi gaggawa don ya gudu, amma wani daga cikin mutane ya cire mayafinsa ya jefa masa. Da ya lura ba makawa za a kama shi sai ya soka wa kansa wuƙar a cikinsa nan take ya mutu.

Sayyadina Umar (RA) ya suma a kan zafin wuƙa da ta ratsa jikinsa. Ana gama sallah shi kuma yana farfaɗowa, sai ya tambaya, jama'a sun yi Sallah? Aka ce masa, eh. Ya ce, babu rabo a cikin Musulunci ga wanda bai yi Sallah ba. Ya umurci Ibnu Abbas ya duba masa wane ne ya soke shi, da ya ji cewa Bamajushe ne sai ya gode Allah a kan ba mai Sallah ne ya soke shi ba. Sannan ya nemi ruwa domin ya yi alwala ya sake Sallah, amma sau uku duk lokacin da ya yi alwala sai zafin ciwo ya buge shi har ya suma, sai a na uku ya samu ya yi sallarsa ta ƙarshe.

Da farko mutane ba su yi tsammanin Umar zai mutu ba sai da wani likita ya zo ya haɗa wani magani ya ba shi ya sha. Da ya sha sai maganin ya fito ta inda aka soke shi a ciki. A nan ne likitan ya umarci Sarkin Musulmi da ya yi wasiyyah. Mutane sun soma kuka a kan jin cewa, za su yi rashin Umar, amma Umar ya hana a yi masa kuka yana mai kafa hujja da hadisin da ya ji daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, ana azabtar da matacce da kukan rayayyu a kansa.

Sahabbai sun kewaye Sarkin Musulmi Umar suna taya shi murnar samun shahada, suna tuna irin kyawawan abubuwan da ya gudanar a rayuwarsa, da ayyukansa a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma adalcinsa a cikin mulkinsa tare da yaba masa, da kuma yi masa fatar alheri. Amma duk a cikinsu babu wanda maganarsa ta yi wa Umar daɗi kamar Ibnu Abbas wanda bayan da ya ƙare jawabinsa Umar ya tambaye shi, za ka shede ni da wannan a gaban Allah? Nan take Ali Ɗan Abu ɗalib ya ce ma Ibnu Abbas, amsa masa ni ma ina tare da kai. Amma dai shi Umar kamar yadda yake cewa, fatar da nike in tsira da ladar jihadina tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wannan aikin naku kuwa in na tashi ba lada ba zunubi to, ba kome.

Umar ya umurci ɗansa Abdullahi ya duba yawan bashin da ake bin sa, sai ya gaya masa cewa, bashin ya kai Dirhami dubu tamanin da shida (Dirh. 86,000). Umar ya ce, ka tattara abin da muka mallaka ka biya bashin, idan bai isa ba ka nemi danginmu Banu Adiyyin su taimaka, idan sun kasa ka nemi ƙuraishawa kar ka wuce su.

Sannan ya umurce shi da ya nemo masa iznin Uwar Muminai A'ishah don yana son a rufe shi a cikin ɗakinta kusa da aminnansa guda biyu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Abubakar Siddiƙ. A'ishah ta tausaya ma Umar ta ce, na aminta na bar masa haƙƙina, amma a da wurina ke nan da na so a rufe ni tare da mahaifina da mijina. Da Umar ya ji wannan bayani sai ya ce da ɗansa, ka sake neman izni idan aka ɗauko gawata za a shigar, domin wataƙila ta ji kunyar rayuwata ne, idan ta sauya ra'ayinta kar a damu, a kai ni maƙabartar sauran Musulmi, ba kome.

Ana haka ne wani saurayi ya shigo domin ya jajanta ma Umar ya ba shi haƙuri, ya kuma yi masa addu'a kamar yadda sauran Musulmi su ke yi. Da ya ba da baya sai Umar ya lura da suturarsa ta zarce haddin Shari'ah, Umar ya sa aka kira shi ya yi masa nasiha yana mai cewa, ka ɗaga zaninka don ya fi tsafta kuma ya fi daidai da yardar Allah.

Allahu Akbar! Haka dai zafin ciwo bai hana Umar yin aikin da ya saba na wa'azi ba. Kuma zai gama mulkin duniyar Musulmi bayan shekaru 12 amma ana bin sa bashin Dirh. 86,000.

Da yamma ta yi, Umar ya lura da kusantowar ajalinsa sai ya umurci ɗansa da ya saukar da kansa daga cinyarsa ya ajiye shi a kan ƙasa don ya yi tawali'u ga Maɗaukakin Sarki. Ya ci gaba da furta kalmomi na neman gafarar Allah har mala'ikan mutuwa ya karɓi rayuwarsa.

Umar bai bar duniya ba sai da ya shata ma Musulmi yadda za su zaɓi wanda zai gade shi, ya kuma bar wasicci mai tsawo ga duk wanda aka zaɓa.

Sahabi Umar ya shugabanci musulmi tsawon shekaru goma da wata biyar da kwana ashirin da ɗaya. Allah SWT Ya kara yarda a gare shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post