Yadda Saudiyya Da Wasu Kasashe Ke Wa Tsuntsun Shaho Fasfo

 A ƙasar Saudi Arabia da sauran wasu ƙasashen Larabawa, ana yi wa tsuntsayen Shaho Fasfo nasu na ƙashin kansu domin tafiye-tafiye ta jiragen sama. Farauta da shaho al'ada ce mai tushe a yankin, kuma Shaho yana da daraja sosai.

Tsuntsun Shaho

Yin fasfo doka ce wacce ke ba tsuntsaye damar ƙetare iyakokin ƙasa da ƙasa don yafiya zuwa farauta, ko lokacin da masu su ke jigilar su. Cibiyar cigaban namun daji ta ƙasa a Saudi Arabiya, tana ba da sabis na lantarki don ba da fasfo ga Shaho, wanda ke taimakawa wajen daidaita zirga-zirgar su ta kan iyakoki. A wasu lokuta, waɗannan tsuntsaye masu daraja suna tafiya tare da masu su a jiragen sama.

Post a Comment

Previous Post Next Post