Yanbindiga Sun Kashe Yansandan Biyar A Jihar Bauchi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Bauchi da ke arewacin ƙasar ta sanar da kashe jami'anta biyar yayin wani kwanton ɓauna da 'yanbindiga suka yi musu.

'Yansandan Nijeriya

W
ata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmad Wakil, ya fitar ta ce dakarun na kan aikin tabbatar da zaman lafiya a rikicin manoma da makiyaya a ƙauyen Sabon Sara na ƙaramar hukumar Darazo lokacin da lamarin ya faru.

Ya ƙara da cewa wasu jami'an biyu sun ji raunuka, yayin da dakarun suka yi nasarar kashe 'yanbindigar da dama.

"Abin baƙin ciki, kwanton ɓaunar ya yi sanadiyyar mutuwar jami'ai kamar haka: DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF),  Amarhel Yunusa (10 PMF), Sufeto Idris Ahmed (10 PMF), Kofur Isah Muazu (AKU)

Post a Comment

Previous Post Next Post