A cewar ƙungiyar, an sace ɗaliban ne a wani hari da aka kai da dare a wata makarantar mishan da ke arewacin ƙasar. ’Yan bindiga sun mamaye makarantar ne suna harbe-harbe, kafin daga bisani su tilasta wa ɗalibai tafiya tare da su cikin duhu.
Ƙungiyar ta ce tserewar ta faru ne bayan ɗaliban sun samu damar gudu a lokacin da masu garkuwa da su suka yi sakaci. Rahotanni sun bayyana cewa ɗaliban sun ruga cikin daji sannan suka ci gaba da tafiya na sa’o’i har zuwa lokacin da suka isa wani gari da ya basu mafaka.
Ƙungiyar Kiristan ta bayyana godiya ga Allah bisa kubutar ɗaliban, tare da jinjinawa mutanen da suka basu taimako da mafaka bayan sun iso cikin dare.
Sai dai ƙungiyar ta nuna damuwa sosai game da ƙara ta’azzarar matsalar tsaro da ta addabi makarantu a arewacin Najeriya. Sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare makarantu da ɗalibai, tare da tabbatar da cewa wuraren karatu sun kasance cikin aminci.
Har yanzu hukumomin gwamnati ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, amma an ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran ’yan bindigar da kuma kare afkuwar makamancin haka a nan gaba.
Wannan lamari ya ƙara yawan jerin sace-sacen dalibai a Najeriya, matsala da ke barazana ga ilimi da tsaron rayuka a wasu jihohin ƙasar.