Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta ƙaddamar da wani mummunan hari kan mayakan IS a arewa maso yammacin Najeriya.
"Dakarun Amurka sun ƙaddamar da hare-hare masu kyau," in ji Trump.Cibiyar sojin Amurka a Afrika daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto.
Shugaban ya zargi ƙungiyar da kai hari tare da kashe Kiristocin da ba su ji ba su gani ba a ƙasar.
A shafinsa na Social Truth, Trump ya wallafa da yammacin Alhamis cewa "a ƙaƙashin shugabancina, ƙasarmu ba za ta bar masu tsattsauran ra'ayin Musulunci sun girmama ba."
Mista Trump bai faɗi lokacin da aka yi kashe-kashen ba da yake magana a kai amma kuma ya yi zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya wanda batu ne da ya yi ta yawo tsakanin masu kaifin ra'ayin Kiristanci a Amurka.
Sakataren harkokin tsaron Amurka Pete Hegseth, ya ce ya gamsu da hadin kai da kuma goyon bayan da gwamnatin Najeriya ta ba su.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce harin wani bangare ne daga cikin hadin guiwar tabbatar da tsaro da aka ƙulla da Amurka.