Wani ƙwararren masanin tsaro da yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai a jihar Sokoto a ranar Alhamis sun kasance harin da bai dace da inda aka nufa ba, domin ba su kai ga lalata ko da wata mafakar ‘yan ta’adda ba.
Makama ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da jama’a ke ta muhawara kan rahotannin da ke nuna cewa sojojin Amurka sun kai farmaki a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) mai tabbaci, Makama ya ce an jefa bama-baman ne a wani wuri da ba a taɓa sanin yana da alaƙa da ayyukan ta’addanci ba, don haka harin bai yi wani tasiri a kan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki a ƙasar ba.
“Ga waɗanda ke neman ra’ayina game da harin Amurka a Sokoto, bama-baman an jefa su ne a wani yanki mai zaman lafiya, kuma ba su yi wani tasiri ba,” in ji shi.
A cewar Makama, yankin da lamarin ya shafa — ƙauyen Jabo — ƙauyen manoma ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto, kuma babu wani tarihi da ke nuna cewa ƙungiyoyin ISWAP, ISIS ko Boko Haram sun taɓa gudanar da ayyuka a yankin.
“Jabo ƙauyen manoma ne a ƙarƙashin Tambuwal, kuma babu ko guda ɗaya da ke nuna ayyukan ISIS ko ISWAP a yankin,” ya ƙara da cewa.
Makama ya jaddada cewa duk da ana maraba da taimakon ƙasashen waje a yaƙin Najeriya da ta’addanci, wajibi ne irin waɗannan hare-hare su kasance bisa ingantattun bayanan sirri, domin kauce wa kai hari a wuraren da ba su da barazana.
“Muna maraba da taimakon Amurka ga Najeriya, amma tabbas Jabo a Sokoto ba wurin da ISWAP, Boko Haram ko ISIS ke aiki ba. Wadannan ƙungiyoyi suna yankin Arewa maso Gabas ne,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa har ma JNIM (wanda aka fi sani da Lakurawa) ba su da sansani a Arewa maso Yamma.
Dangane da raɗe-raɗin da ke danganta harin da batun rikicin addini, Makama ya ce yankin ba ya barazana ga Kiristoci, inda ya bayyana cewa yawancin mazauna yankin Musulmi ne kuma su ma ’yan fashin daji ne ke addabarsu.
“Yankin da aka kai harin kusan kashi 98 cikin 100 Musulmi ne, kuma ba shi da wata barazana ga Kiristoci. Abin da ke faruwa shi ne ‘yan bindiga na gallaza wa Musulmi,” in ji shi.
Duk da sukar da ya yi kan inda aka kai harin, Makama ya jaddada cewa ci gaba da matsin lamba na soja a kan ƙungiyoyin ta’addanci abu ne mai muhimmanci.
“Duk da haka, irin waɗannan hare-hare da ma waɗanda za su biyo baya abin maraba ne, domin za su aika saƙo mai ƙarfi,” ya kammala.